Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya soma jawabinsa da tunatar da mahalarta cewa yau 20 ga Safar ya cika kwanaki arba'in da shahadar Imam Husaini (A.S), iyalansa da sahabbansa. Ya bayyana cewa, ziyarar Arba'in, wani zaunannen lamari ne a addinin Musulunci tun daga shekara ta 61 bayan hijirar Manzon Allah (S), lokacin da Sahabi Jabir bn Abdullahi Al-Ansari ya fara ziyartar kabarin Imam Husaini (AS) bayan aukuwar waƙi'ar Karbala. Ya ziyarci kabarin, ya yi kuka tare da kiran masoyinsa, duk da cewa ba zai iya jin amsawarsa ba.
Jagora (H) ya naƙalto hadisin Jabir (RA) cewa, ya ji Manzon Allah (S) yana cewa: "Wanda ya so wasu mutane, za a tashe shi tare da su. Wanda ya so aikin wasu mutane, za a haɗa shi da su a ayyukansu.” Don haka ya ce, “Ku shaida, muna son Husaini, muna son iyalan Husain, muna son sahabban Husaini; muna ƙaunar su da ayyukansu, kuma muna roƙon Allah Ya tashe mu tare da su."
Ya yi tsokaci kan yadda ake gudanar da tarukan Arba'in a wannan rana a Karbala, inda ya jaddada muhimmancin ranar, yana mai cewa Arba'in na daga cikin alamomin mumini. Ya kawo hadisin Imam Hasan al-Askari (AS) cewa, daga cikin alamomin mumini biyar akwai ziyarar Arba'in na Imam Husaini (AS), yana mai bayyana cewa ana yin wannan ziyara ko a kusa ko daga nesa.
Jagora ya kuma nuna yadda lamarin Arba'in ya bazu a duniya, inda ake raya wannan rana a ƙasashe daban-daban na Gabas da Yamma. Ya ce, wannan yana daga cikin raya al'amuran Ahlul Baiti (AS).
Haka kuma ya tuna da jawabin Sayyida Zainab (AS) a gaban Yazidu, inda ta bayyana masa cewa ba zai taɓa iya shafe ambaton Ahlul Baiti ba. Jagora ya ce, a yau ana ci gaba da tuna al'amarin Imam Husaini (AS), tare da yin Allah-wadai da Yazidu (LA).
Ya ce: "In ka ji ana tsine wa tsinanne ka ji haushi, kai ma tsinanne ne. Domin ba wanda zai ji haushin an tsine wa tsinanne sai tsinanne."
Jagora ya bayyana cewa, Allah Ya sanya Ahlul Baiti (AS) su zama ma'aunin gane gaskiya. Ya kuma tuna da matsayin Imam Husaini (AS) lokacin da ya kasance tsakanin zaɓin bin azzalumai ko kuma shahada, inda ya zaɓi shahada. Ya nanata kalmar "Haihata Minazzilla", yana mai cewa, mabiyan Imam Husaini ba za su taɓa miƙa wuya ga azzalumai ba.
Shaikh Zakzaky ya ce: "Allah Ya yi mana daraja, Ya ɗaukaka mu, ba za mu yarda mu rayu a ƙarƙashin ƙasƙantattu ba."
Jagora ya bayyana cewa, makarantar Imam Husaini (AS) ta koyar da darussa masu yawa, kuma ita ce ta samar da Juyin Juya Halin Musulunci na Iran shekaru 47 da suka gabata. Ya ce, duk da takunkuman da aka ƙaƙaba wa Iran tsawon shekaru, hakan ya haifar da ci gaba da ƙarfafa ƙasar, har ta kai ga kare kanta daga maƙiyanta, wanda ya bayyana a matsayin abin alfahari ga Musulmi.
Ya ce: "Wannan natijar makarantar Imam Husaini (AS) ce ta sadaukarwa. Mun gwammace shahada da miƙa wuya; abin da Imam Husaini ya koyar ke nan."
Jagora ya ƙara da cewa nasara daga Allah tana tare da masu bin tafarkin Imam Husaini (A.S), Imam Ali (A.S), Manzon Allah (SAW) da Imam Mahdi (ATFS). Ya jaddada cewa, Imam Mahdi (ATFS) shi ne shugabansu, kuma zai bayyana, addinin Musulunci zai mamaye duniya, mabiyansa kuma za su koma daga ƙaranci zuwa yawa, daga ƙasƙanci zuwa ɗaukaka.
Jagora (H) ya kuma tuna da shahidan tattakin Arba'in da aka kashe a harin bam a hanyar Kano a shekarar 1435H, inda aka samu shahidai 21. Haka kuma ya taɓo azzalumai masu takurawa, yana mai cewa: "Ko ku yi harbi, ko ba ku yi ba, ba za mu daina (ayyukanmu na addini) ba."
A ƙarshen jawabinsa, Jagora ya soki yadda shugabannin ƙasar ke nuna halin ko-in-kula da rayuka da walwalar al'umma, amma ya ce, hakan ba zai dawwama ba.
Ya ce: "Ku bar ganin kuna ganin mu ba mu da yawa yanzu. Muna wakiltar dukkan al'ummar nan ne, kuma da sannu za ku ga al'umma baki ɗaya tare da mu. Insha Allahu, wannan alƙawarin Allah ne cewa addinin nan zai tabbata daram-dam! Kamar ma ya tabbata".
Jagora ya kammala da addu'ar Allah Ya maida kowa gida lafiya.
An fara taron tun misalin ƙarfe 10:00 na safe da ma'atham daga Ittihadus Shu'ara. Daga bisani Harisawa da Intizar suka gabatar da 'display', yayin da IM Production suka yi tamsiliyyar waƙi'ar Karbala kafin Jagora (H) ya gabatar da jawabinsa. An kammala taron da yammacin wannan rana.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
20/Safar/1448
04/08/2026
Ra'ayinka